Bnagaren siyasa da zamantakewa, yanzu ana shirin gudanar da wani zaman taro na tunawa da jagoran juyin juya halin muslunci a kasar Iran marigayi Ayatollah Ozma Imam Khomenei (RA) a birnin Sarayevo fadar mulkin kasar Bosnia, wanda zai samu halartar mabiya addinin muslunci na kasar ta Bosnia.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, yanzu ana shirin gudanar da wani zaman taro na tunawa da jagoran juyin juya halin muslunci a kasar Iran marigayi Ayatollah Ozma Imam Khomenei (RA) a birnin Sarayevo fadar mulkin kasar Bosnia, wanda zai samu halartar mabiya addinin muslunci na kasar ta Bosnia da wasu kasashen gabacin nahiyar turai.
Imam Khumaini (r.a) wanda ya kafa jamhuriyar Musulunci ta Iran mutum ne wanda ya sadaurar da kansa da rayuwarsa domin ganin ya ceto da al'umma da kuma kai ta ga daukaka. Kuma abinda ya ke faruwa a wannan lokacin a cikin kasashen larabawa na yunkurin da al'ummu su ke yi domin 'yantar da kawunansu daga azzaluman shugabanni, yana sake dawowa da mutane tunani akan Imam khumaini. Kuma a wannan lokacin a duk inda ake yin tattaunawa dangane da sauyin da ya ke faruwa acikin kasashen musulmi, ana ambaton juyin juya halin Musulunci na Iran bisa jagorancin Imam khumaini a matsayin harsashi da mafari.
Su kansu al'ummar musulmi suna danganta tunanin sake kowama ga riko da adinin Musulunci da koyarwarsa mai girma a cikin wannan zamanin zuwa ga Imam Khumaini. Dr. Muhammad Farraly wanda manazarci ne Musulunci dan kasar Masar yana fadin cewa a cikin wata makalarsa.
Farkawar Musulunci wata kalma ce da ta samo asali da kuma yaduwa bayan cin nasarar juyin Musulunci bisa jagorancin Imam Khumaini (RA).
802248