IQNA

Bincike Kan Raya Dare Da Kratun Kur'ani Tare Da Makarantan Masar A Karbala'a

15:55 - June 12, 2011
Lambar Labari: 2136906
Bangaren kasa da kasa; a daren jiya ashirin ga watan Khurdad shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya an gudanar da bincike kan raya dare da karatun kur'ani mai girma kuma an samu halartar fitattun makaranta kur'ani daga kasar maser da suka hade a hubbarin Aba Abdullahi Huseini (AS) da ke birnin Karbala'a.



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a daren jiya ashirin ga watan Khurdad shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya an gudanar da bincike kan raya dare da karatun kur'ani mai girma kuma an samu halartar fitattun makaranta kur'ani daga kasar maser da suka hade a hubbarin Aba Abdullahi Huseini (AS) da ke birnin Karbala'a.Wadannan fittatun makaranta sun yi bayani dalla dalla kan muhimmancin karatun kur'ani da kuma yadda duk wanda zai raya dare da karatun kur'ani zai kasance da samun kansa cikin farin ciki da walwala da kuma yin bayani kan irin falalar da ke tattare da karatun kur'ani musamman raya dare guda da karatun kur'ani.

806255
captcha