IQNA

Zangon Koyar Da Kur'ani Ga Yara Kanana A Tataristan

15:52 - June 20, 2011
Lambar Labari: 2141346
Bangaren kula da harkokin kur'ani: a daidai wannan lokaci na shiga hutun bazara na makarantu za a fara zangon karatun kur'ani mai girma a masallatan yankin Almetyevsk na jamhuriyar Tataristan kuma wannan zagon ya kebantu ne ga yara kanana da matasa na kasar.


Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a daidai wannan lokaci na shiga hutun bazara na makarantu za a fara zangon karatun kur'ani mai girma a masallatan yankin Almetyevsk na jamhuriyar Tataristan kuma wannan zagon ya kebantu ne ga yara kanana da matasa na kasar.wannan zagon karatu daga ranar sha shida zuwa ashirin da shida ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tsi'in hijira shamsiya aka gudanar ga yara kanana inda yara talatin da biyar suka halarci wannan zangon karatun kur'ani mai girma.


811188

captcha