Bangaren kur’ani, gidan talabijin din kasar Iran zai watsa shirin gasar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa da za a fara gudanarwa a kasar, tare da halartar malaman addinin daga kasashen duniya musamman ma na musulmi da kuma larabawa, gami da wakilai na cibiyoyin kur’ani na kasa da kasa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizoan bayyana cewa, gidan talabijin din kasar Iran zai watsa shirin gasar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa da za a fara gudanarwa a kasar, tare da halartar malaman addinin daga kasashen duniya musamman ma na musulmi da kuma larabawa, gami da wakilai na cibiyoyin kur’ani na kasa da kasa da za su sanya ido kan yadda gasar za ta gudana.
Wani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo na le-coran an bayyana cewa, an saka tarjamar kur’ani mai tsarki a cikin shafin yanar gizo a cikin harshen farasanci, tare da karatun kur’ani mai tsarki daga fitattun makaranta na duniyar musulmi, da nufin kara fadada ayyukan kur’ani a shafukan yanar gizo da ake ziyarta koina cikin duniya.
Bugu da kari kan tarjamar kur’ani mai tsarki a acikin harshen faranci dake cikin wannan shafi na yanar gizo, za a iya sanin wasu abubuwan da suka shafi kur’ani, kamar sanin adadin ayoyin da ke cikin sura, ko kuma dalilan safkar ayoyi da kuma tafsirin ma’nar wasu kalmomin kur’ani, da suke bukar bayani ta yadda mai karatu ba zai sha wahala wajen gane ma’narsu ba.
Kamar dai kowace shekara gidan talabijin din kasar Iran zai watsa shirin gasar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa da za a fara gudanarwa a kasar, tare da halartar malaman addinin daga kasashen duniya musamman ma na musulmi da kuma larabawa, gami da wakilai na cibiyoyin kur’ani na kasa da kasa, domin sauran mutane na cikin gida su gane wa idanunsu yadda gasar take gudana.
812545