Bangaren kur'ani, za a gudanar da wani shiri na tilawar kur'ani mai tsarki a hubbaren Sayyid Abdulazim da ke garin Rai a birnin Tehran, tare da halartar dalaiban makarantun kur'ani mai tsarki da kuma malamai gami da wakilan cibiyoyin bunkasa ayyukan kur'ani na kasa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, za a gudanar da wani shiri na tilawar kur'ani mai tsarki a hubbaren Sayyid Abdulazim da ke garin Rai a birnin Tehran, tare da halartar dalaiban makarantun kur'ani mai tsarki da kuma malamai gami da wakilan cibiyoyin bunkasa ayyukan kur'ani na kasa baki daya.
Babban malamin jami'ar Azhar ta kasar Masar Sheikh Ahmad Tayyib ya kira ga dukkanin malaman jami'ar Azhar da sauran malaman addinin muslunci ta kasashen duniya da su yada sahihiyar koyarwar addinin mulunci a duniya baki daya.
Shehin malamin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke gabatar da wani jawabi a gaban wani bababn taro na malaman addinin muslunci na duniya da aka gudanar a birnin Alkahira fadar mulkin kasar ta Masar, wanda ya samu halartar masana daga sassa daban-daban na kasashen duniya, musamman ma kasashen musulmi da na larabawa.
813219