Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci tai ran ne ya watsa rahoton cewa; Said Tusi fitaccen makarancin kur'ani an girmama shi a rana ta uku ta fara gasar karatun kur'ani mai girma ta kasa da kasa da ake ci gaba da gudanarwa a nan jamhuriyar musulunci ta Iran a wannan gasa ta kasa da kasa karo na ashirin da takwas.Wannan mataki na girmama tsaffin makaranta kur'ani mai girma zai kara fito da irin wannan gasa ta kasa da kasa da kuma girma makaranta kur'ani da suka gabata da kuma karawa duk wani makarancin kur'ani karfin guiwa da jinjina masa.Kuma wannan wani babban mataki ne da sabon salo a wannan gasar karatun kur'ani ta kasa da kasa.
818741