Bangaren kur’ani, wakilin kasar Iran a gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa da ake gudanarwa a birnin Tehran, ya bayyana cewa ya kwashe tsawon shekaru har goma sha biyu yana halartar gasar kur’ani a duniya kafin ya zo a matsayi na farko.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, awani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo an bayyana cewa, Murteza Muhammad Najad wakilin kasar Iran a gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa da ake gudanarwa a birnin Tehran, ya bayyana cewa ya kwashe tsawon shekaru har goma sha biyu yana halartar gasar kur’ani a duniya kafin ya zo a matsayi na daya a cikin gasar.
Ya ci gaba da cewa babban abin da ke da muhimmanci ga duk wani wanda yake makarancin kur’ani ne ko kuma mahardaci, shi ne ya mayar da hankali ga abin da yake yi, tare da yin komai domin Allah madaukakin sarki, domin kuwa manufar gasar ita ce kara bayyana matsayin kur’ani mai tsarki ba matsayin da mutum zai zo ba, domin kuwa raya lamarin kur’ani shi ne manufar gasa, duk kuwa da cewa dabi’a ce ta mutum yana son ya yi kwazo a cikin kowane lamari.
wakilin kasar Iran a gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa da ake gudanarwa a birnin Tehran, ya bayyana cewa ya kwashe tsawon shekaru har goma sha biyu yana halartar gasar kur’ani a duniya kafin ya zo a matsayi na farko.
818962