Bangaren kur'ani, an far agudanar da gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta kasar India, tare da halartar makaranta daga sassa daban-daban na kasar, inda suke karawa da juna, daga karshe kuma za asanar da sunayen dukkanin wadanda suka nuna kwazo.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar al'adu ta 'yan sunna a kasar India an bayyana cewa, an far agudanar da gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta kasar India, tare da halartar makaranta daga sassa daban-daban na kasar, inda suke karawa da juna, daga karshe kuma za asanar da sunayen dukkanin wadanda suka nuna kwazo, tare da ba su kyutuka na musamman.
Taron an bude shi ne a ranar Asabar da ta gabata tare da karanta jawabin jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Iran Ayatullahil Uzma sayyid Ali Khamina'I.da ya kunshi bayani kan harshen damo da kasashen yammacin duniya suke yi kan ma'anar ta'adanci da yake da shi. Har ila yau a ranar ta farko shuwagabannin kasashen Iran, Pakistan, Sudan, Afghanistan, Iraki, da kuma Tajikistan sun bayyana mahangar gwamnatocinsu game da batun ta'adanci da muhimmancin yin aiki tare domin kawo karshensa.
A rana ta biyu na taron ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Akbar salihi ya yi bayani ga mahalarta taron inda ya jinjinawa manyan baki da suka fito daga kasashe 60 na duniya kana ya nuna fatansa na ganin sakamakon wannan taron ya samar da fahimta da tunani daya ta yadda za'a yi aiki tare da zai bada fa'ida mai kyau wajen yaki da ta'adanci, har ila yau ministan ya nuna irin asarorin da kasar Iran ta samu sakamakon ayyukan ta'adanci, don haka ne ma take All.. wadarai da dukkan nauo'in ayyukan ta'adanci, kuma duk wani yin amfani da karfi kan mutane da basu da laifin zaune balle na tsaye abin zargi ne kuma ba za'a taba amincewa da shi ba.
819579