IQNA

Kyakyawar Niya da Hakuri Su ne Matakin Farko Na Hardar Kur'ani

15:59 - July 10, 2011
Lambar Labari: 2152003
Bangaren kasa da kasa; duk wani mai son yin harder Kur'ani mai tsarki bayan niyar mai tsarki ta kusantar Allah dole ne ya kasance ya kebantu da abubuwa biyu na farko ikhlasi sai kuma na biyu hakuri da juriya a tsawon lokacin harda.


Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran net a watsa rahoton cewa; duk wani mai son yin harder Kur'ani mai tsarki bayan niyar mai tsarki ta kusantar Allah dole ne ya kasance ya kebantu da abubuwa biyu na farko ikhlasi sai kuma na biyu hakuri da juriya a tsawon lokacin harda.Abdulwahid Muhammad Yusif ma hardacin kur'ani dan shekaru ashirin da uku dan kasar Keniya day a halarci gasar karatun kur'ani da harda ta kasa da kasa karo na ashirin da takwas a nan Tehran awata tattauanawa da kamfanin dillancin labarai na ikna ya bayyana cewa;buri kar ya kasance harder kur'ani mai tsarki ko ayoyin kur'ani da karanta su a'a burin ya kasance a kullum muna tare da maganar allah a duk lokaci da yanani na rayuwarmu muna tare da Allah saboda haka harder kur'ani mu hada shi da sanin ma'ana ta hakika ta abin da muke karantawa da kuma aiki da shi a kullum.

821413

captcha