Bangaren kasa da kasa, matar tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Masar ta yi barazanar cewa idan shugabannin kasashen larabawa suka yi wata Magana kan shari'ar mijinta to za ta tona asirinsu kan abubuwan da suka yi ta kullawa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto rahoto dake cewa, matar tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Masar ta yi barazanar cewa idan shugabannin kasashen larabawa suka yi wata Magana kan shari'ar mijinta to za ta tona asirinsu kan abubuwan da suka yi ta kullawa a lokacin da yake kan mulkin kasar Masar.
A zanatawar da ta hada kamfanin dilalcin labaran kur'ani na iqna da daya daga cikin masu nazari da bincike kan harkokin siyasa da ke kai da komowa dan asalin kasar Bahrain Jawad Abdulwahab ya bayyana cewa, azzaluman shugabannin larabawa suna matukar jin tsron cewa uffan dangane da shari'ar Husni Mubarak, domin kuwa su ma abin da ya yi ne suke yi.
Susan matar tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Masar ta yi barazanar cewa idan shugabannin kasashen larabawa suka yi wata Magana kan shari'ar mijinta to za ta tona asirinsu kan abubuwan da suka yi ta kullawa na makirci kan musulmi da sauran larabawa.
839458