Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, madaukakin sarki a koda yaushe yana tare da bayinsa, kuma yana sauraren addu’arsu, kuma yana karba musu idan sun roke shi, a kan haka kada mu yi saku-saku da addu’a, a kowane lokaci. Bayan haka kuma za mu fahimci cewa shi Allah ne yake kiran bayinsa da su roke shi saboda yawan rahamarsa da tausayinsa, da kuma yadda a koda yaushe yake son bayinsa da alkhairi, kuma karba wannan kira na Allah wato rokonsa da yin addu’a, yin hakan yana tattare da shiryar ubangiji.
Daga cikin ka’idoji da dokoki na azumi addinin muslunci ya gindaya wa musulmi a cikin watan ramadan, a lokacin azumi haramun ne su kusanci matayensu, kamar yadda haramun ne su ci abinci ko abin sha, har sai bayan shan ruwa, amma kafin safkar wannan ayar kusantar mataye ya kasance cikin abubuwan da aka hana a cikin watan ramadan baki daya har ma cikin dararensa.
Lamarin da ya yi wa wasu daga cikin musulmi matukar wahala, inda suka fadi wannan jarabawa ta ubangiji, amma daga bisani Allah ya safkar da wannan aya kuma ya yi musu afuwa kan hakan, kuma ka halasta musu kusantar mataye a daga bayan shan ruwa har zuwa kafin fitowar alfijir, koda yake wannan hukunci ya takaitu ne ga wadanda ba suna cikin i’itikafi ne ba ne a masallaci, domin su hakan bai halasta gare su ba.
Wannan aya mai albarka ta siffanta mata a matsayin tufa ga maza, kamar yadda mazaje suke a matsayin tufa ga matayensu, tofa bisa ga al’ada tana rufe tsiraici da aibi, tana kuma kawata wanda ya saka ta. A kan haka ne kur’ani ya bayar da wannan misali, domin kuwa ma’aurata suna matsayin tufa ne ga junansu, kowanne dayansu yana taimaka dayan ne, yana yi masa nasiha, yana nuna masa gaskiya, ya shiryear da shi zuwa ga abin da Allah ke so domin ya aikata, da nusar da shi abin da Allah ba ya so domin kaurace masa, sakamakon kaunar juna da tusayi da ke tsakaninsu.
840230