Bangaren kur'ani, makonni kenan ana fama da yinwa kasar Somalia kuma da dama daga cikin mutane da abin ya shafa asuna bukatar taimakon gaggawa , to menen al'ummar kur'ani ta yi domin taimakon musulmin kasar Somalia da suke fama da wannan matsala.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, makonni kenan ana fama da yinwa kasar Somalia kuma da dama daga cikin mutane da abin ya shafa asuna bukatar taimakon gaggawa , to menen al'ummar kur'ani ta yi domin taimakon musulmin kasar Somalia da suke fama da wannan matsala wadda take lakume rayukan kanan yara.
A cikin wani sako na sauti da gidan rediyon kasar Libya ya watsa a cikin daren da ya gabata, shugaban kasar Libya Mu'ammar Kadaffi ya yi kira ga magoya bayansa da su tashi tsaye haikan domin kwato illahirin garuruwan da suke a hannun 'yan tawayen kasar.
A cikin jawabin nasa, kanar ya bayyana cewa ''Nan ba da jimawa ba ne zamu kwato sauran yankunan kasar da 'yan tawaye masu samun goyon bayan kungiyar tsaro ta Nato suke rike da su''. Wannan jawabi na Kaddafi ya zo ne a daidai lokacin da rahotanni ke cewa 'yan tawayen na ci gaba da garzawa zuwa birnin Tripoli bayan da suka kwace garuruwa da dama daga hannun sojojin.
Tun a cikin watan Maris da ya gabata ne dai kungiyar tsaro ta ato da kuma 'yan tawayen suke ci gaba da gwabaza fada da sojojin kasar ta Libya a kokarin da suke na kawar da Kanar daga kan karagar mulkin kasar wacce shi ma ya dare a kanta ta hanyar juyin mulki a shekara.
845332