IQNA

An Yi Bayanin Ayyukan Kur'ani Mai Tsarki Da Masallatai A Baje Kolin Kur'ani

16:41 - August 21, 2011
Lambar Labari: 2174765
Bangaren kur'ani, abu mafi bayyana daga cikin muhimamn lamurran da suka danganci ayyukan kur'ani da masallatai a wannan shekara ta 90, shi ne yadda aka samara da sabbin abubuwa da suka bayyana hanoron musulmi wajen raya kur'ani.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an sheda cewa, Wasu daga cikin ahlul kitab a lokacin ma'aki duk da masaniyar da suke da ita ta zuwan kur'ani mai tsarki daga Allah madaukin sarkin bayan littafan Attauara da Injinla, amma ba a shirye suke ba su yi imani da manzon karshe, kuma su karbi kur'ani mai tsarki a matsayin littafin da ya zo daga Allah madaukakin sarki.

Wannan aya ta ba su amsa da cewa, a tsawon tarihi Allah yana aiko annabawa domin shiryar da mutane, wasu daga cikinsu ana ba su sha'ri'a da littafi, dukaknin wadannan annabawa sun gasgata junasu, saboda dukakninsu daga Allah ubagiji daya suke, kuma sakonsa ne suke isarwa ga 'yan adam. A kan haka babu wani abun mamaki, domin kuwa ubangijin da ya safkar da Attauara ga annabi Musa ya safkar da Injila ga annabi Isa, shi ne ya safkar da kur'ani ga manzon Muhammad (SAW)

Saboda haka wannan aya ta gaya musu cewa idan da gasket suna neman gaskiya ne, to wajibi ne su yi iani da annabi Muhammad da sakon da ya zo da shi daga Allah,duk lokacin da muka shiga dimuwa da fangima, to ku koma zuwa ga kur'ani mai tsarki, domin shi wasila ne na banbamce gaskiya da karya.

Daya daga manyan ayyukan zalunci shi ne rafkana daga ubangiji, alhali babu wani lokaci da mutum ba ya karkashin ikon ubangiji, kuma yana gani da sauraren dukkanin ayyukan mutum, ba ma mutum ba wanda adadinsa ko alama bai kai halittun Allah da ke cikin sammai da kassai ba, wadanda su ma Allah yana tare da su, yana da masaniya kan dukkanin abin da suke yi.
Bi hasali ma shi ne ke ikon tafiyar da su baki daya, babu abin da ke buya ga Allah, a cikin sammai da kassai da abin da ke tsakaninsu, hatta ma jariri da ke cikin mahaifa samuwarsa tana hannun Allah, shi ne yake tsara halittar jinjiri a cikin mahaifa har ya kai lokacin da zai gama girma a haife shi, ya raya shi ya kare shi, lallai Allah shi ne mai hikima.

846560
captcha