IQNA

Kur'ani Mai Rubutu Launi Na Kara Fahimta Da Dangantaka Da Ayoyi

14:28 - October 05, 2011
Lambar Labari: 2199559
Bangaren kasa da kasa: burin na na rubuta da buga kur'ani mai dauke da rubutun launi launi don samin masu karatu da fahimtar ayoyin kur'ani cikin sauri da sauki day a kumshi dukan bangarori na shekaru kama daga kananan yara da kuma matasa da wadanda shekarun ya yi sama.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna ne da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; burin na na rubuta da buga kur'ani mai dauke da rubutun launi launi don samin masu karatu da fahimtar ayoyin kur'ani cikin sauri da sauki day a kumshi dukan bangarori na shekaru kama daga kananan yara da kuma matasa da wadanda shekarun ya yi sama.Muhammad Ali Sarin wani marubucin Kur'ani dan kasar Turkiya ne ya bayyana haka a wata tattauanwa day a yi da kamfanin dillancin labarai na Ikna tare da kara bayyana cewa wannan shi ne karon farko a duniya da aka fassara da tarjama kur'ani a cikin yare uku a hade ,yarerukan kuwa sune Istambul da Farisanci da larabci kuma cikin kala domin kawo sauki wajan fahimtar ayoyinsa.

873011

captcha