Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na tashar talabijin din rasid cewa, gwamnatin Saudiyya ta kashe wasu matas uku a gabacin kasar da suke gudanar da zanga-zangar nemna sauyi ta hanyar yin amfani da harsai masu rai a kansu lamarin da ya ya zuwa yake kara fusata mutane domin ci gaba da neman hakkokinsu da mahukunatn kasar suke dannewa.
Rahotannin da suke fitowa daga kasar Saudiyya suna nuni da cewa jami'an tsaron kasar sun bude wuta kan masu zanga-zangar a yankin Al-Shuwaika da ke garin Qatif lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum guda da kuma raunana wasu.
Jami'an tsaron kasar Saudiyyan sun kai hari kan masu zanga-zangar ne ta hanyar harba harsasai masu kisa lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar wani matashi dan shekaru 19 a duniya mai suna Nasir al-Mahaishi, sannan kuma suka ci gaba da killace yankin da kuma kama duk wanda suka samu da kuma ci gaba da musguna musu.
Rahotannin sun kara da cewa al'ummar yankin sun tare taruwa don yin Allah wadai da amfani da karfin da jami'an tsaron Saudiyyan suke yi da kuma kin mika gawan wannan saurayin ga iyalansa..
Kungiyar neman sauyi na yankin al-Awamiyya na kasar Saudiyya, cikin wata sanarwa da suka fitar sun kirayi al'ummar yankin da su fito kwansu da kwarkwatansu wajen jana'izar wannan saurayin, lamarin da ake ganin yana daga cikin dalilan da ya sanya mahukutan Saudiyya kin ba da gawar tasa don gudun wannan taro na jama'a.
903990