Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na jaridar yaum sabi ta kasar Masar cewa, sakamakon farko na zaben da aka gudanar da a kasar Masar na nuni da cewa kungiyar ‘yan uwa musulmi ne kan gaba a zaben da aka gudanar a kasar wanda shi ne irinsa na farko da aka gudanar bayan faduwar gwamnatin Husni Mubarak tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zabe ya bayyana matsayin mutanen kasar kan demokradiya, domin kuwa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar ta bayyana cewa mutanen da suka shiga zaben sun haura kashi saba’in cikin dari, kuma sabuwar jam’iyar ikhwan ce kan gaba, duk kuwa da cewa akwai masu sukar kungiyar saboda azarbabain da take nunawa da neman mulki karara, maimakon goyon bayan matasan da suke neman majalisar soji ta gaggauta safka.
Tun a cikin makonni biyu da suka gabata ne matasan da suka yi juyi a masar suka koma babban dandalin tahrir da ke tsakiyar birnin Alkahira, sakamakon matakin da majalisar soji ta dauka na neman yin ta zarce bayan da suka karbi mulki daga Mubarak tun a cikin watan Fabrairun da ya gabata.
Yanzu haka dai sakamakon farko na zaben da aka gudanar da a kasar Masar na nuni da cewa kungiyar ‘yan uwa musulmi ne kan gaba a zaben da aka gudanar a kasar wanda shi ne irinsa na farko da aka gudanar bayan faduwar gwamnatin Husni Mubarak babban aminin yahudawan sahyuniya.
908767