IQNA

Ministan Kula Da Harkokin Al’adu Ya Jadda Muhimmancin Aikin Kafofin Sadarwa

18:56 - December 20, 2011
Lambar Labari: 2242349
Bangaren kasa da kasa, ministan kula da harkokin al’adu na jamhuriyar muslunci ta Iran ya jadda wajabcin fadada ayyuka tare da kafofin yada labarai na kasashen ketare domin tona asirin makiya muslunci kan makircin da suke kullawa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya naklato daga shafin sadrawa na yanar gizo cewa, a yau ne ministan kula da harkokin al’adu na jamhuriyar muslunci ta Iran ya jadda wajabcin fadada ayyuka tare da kafofin yada labarai na kasashen ketare domin tona asirin makiya muslunci kan makircin da suke kullawa domin kawo cikas ta kowace fuska.
Bayanin ya ci gaba da cewa ministan ya bayana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a gaban taro wanda hukumar raya al’adu da ilmin muslunci ta kasa da kasa ta shirya kan harkokin sadarwa a karo na bakwai a birnin Algiers na kasar Algeria, tare da halartar jamia’io daga kasashen muslmi da na larabawa.
Ministan kula da harkokin al’adu na jamhuriyar muslunci ta Iran ya jadda wajabcin fadada ayyuka tare da kafofin yada labarai na kasashen ketare domin tona asirin makiya muslunci kan makircin da suke kullawa kan addinin muslunci.
Tun kafin wannan lokacin dai Iran ta sha alwashin ci gaba da fadada harkokin sadrawata domin bayyana hakinanin abin da yake faruwa tsakaninta da makiya, maimakon ji daga bangaren makiyawa kawai.
918650
captcha