Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-intiqad cewa, Al'ummar kasar Bahrain na ci gaba da gudanar da zanga-zangar lumana a dukkanin fadin kasar domin neman sauyi na demokradiyya a kasar, duk kuwa da irin matakan da mahukuntan kasar suke dauka wajen murkushe su da karfin tuwo.
Rahotanni daga kasar ta Bahrain sun habarta cewa, dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zangar lumana a daren jiya a yankunan Markha, Sitra, Barbad, Kasr, akkar, da kuma Sarifiyya, inda suki ta rera taken neman sauyi a cikin harkokin siyasar kasar, jami'an tsaro a cikin kayan sarki sun afka kan masu zanga-zangar, tare da antaya musu barkonon tsohuwa da kuma duka da kulake, haka nan kuma sun awon gaba da wasu daga cikin fararen hula masu zanga-zangar.
A bangare guda kuma wasu daga cikin wadanda aka saka daga gidajen kurkun masautar Bahrain sun sheda cewa, an gana musu azaba mai tsanani, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar wasu daga cikinsu, wasu kuma sassan jikinsu sun nakasa, sun yi Allawadai da kasashen larabawa kan yadda suka yi gum da bakinsu kan ta'asar da mahukuntan Bahrain suke tafkawa kan fararen hular kasar masu neman sauyi, musamman ma Saudiyya wadda ta aike da dakarunta domin murkushe masu neman sauyi a kasar ta Bahrain.
921458