Bangaren kasa da kasa; Wata kungiyar musulunci a arewacin Amerika mai suna ICNA a takaice a kokarinta na rusa bakin kollon da ake yi wa addaninin musulunci da musulmi a wannan kasa da isar da sakon na hakika day a cancanci addini da musulmi suna raba kur'ani da wasu bayanai da suka danganci addinin musulunci da kur'ani kyauta.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsari a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Wata kungiyar musulunci a arewacin Amerika mai suna ICNA a takaice a kokarinta na rusa bakin kollon da ake yi wa addaninin musulunci da musulmi a wannan kasa da isar da sakon na hakika day a cancanci addini da musulmi suna raba kur'ani da wasu bayanai da suka danganci addinin musulunci da kur'ani kyauta.Muhammad Mazhar daya daga cikin mambobin wannan kungiya ta musulunci a arewacin Amerika ya bayyana cewa: mummunar fasssarar da ake yi wa addinin musulunci da kuma bashi mummunan siffa dab a ta dace das hi bad a hakan ya sa a ke kollon musulmi a yammacin Turai musammam a kasa kamar amerika ya tilasta masu daukan wannan matsayi da mataki na rarraba kur'ani mai girma kyauta da duk wani mai bukata a Amerika . Har ila yau suna gabatar da bayanai na hakika kuma gamsarsu dangane da kur'ani mai tsari da kuma abubuwan day a kumsa domin canja masa ra'ayi da mummunan kollon da suke yi wa addaninin musulunci da kuma littafin addainin wato Kur'ani mai girma.
930884