Bangaren kasa da kasa, shugaban majalisar dokokin kasar Masar Hamad Sa’ad ya mayar da da sakon taya murna da majalisar dokokin haramtacciyar kasar Isra’ila ta aike masa tare da bayyana cewa ba su yin na’am da duk wani sakon taya murna daga wannan haramtacciyar kasa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Almanar cewa, shugaban majalisar dokokin kasar Masar Hamad Sa’ad ya mayar da da sakon taya murna da majalisar dokokin haramtacciyar kasar Isra’ila ta aike masa tare da bayyana cewa ba su yin na’am da duk wani sakon taya murna daga wannan haramtacciyar kasa da ke dasawa da tsohuwar gwamnatin kama karya.
A bangare guda kuma ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na jaridar Al-ra’ay ta kasar Masar cewa, wahabiyawan kasar Masar sun kawafa wani kwamiti na umurni da kyakkyawa da kuma hani daga mummuna wanda da dama daga cikin al’ummar kasar suka yi Allawadai da shi kamar yadda ita ma jami’ar Azhar kan kafa wannan kwamiti domin aiwatar da manufar wata kasa da ke bin akidar wahabiyanci da ke yankin.
Al’ummar kasar Masar dai suna zargin gwamnatin kasar saudiyya da hannu kai tsaye wajen taimaka wa ‘yan salafiyya da ke bin akidar wahabiyanci, kuma abin da yake faruwa yanzu haka a kasar ya tabbatar da wannan aniya ta wahabiyawan.
Jama’ar wahabiyawan kasar Masar sun kawafa wani kwamiti na umurni da kyakkyawa da kuma hani daga mummuna wanda da dama daga cikin al’ummar kasar suka yi Allawadai da shi kamar yadda ita ma jami’ar Azhar kan wannan batu.
941371