IQNA

Yahudawan Sahyuniya Na Kira Da A Saki Tsohon Shugaban Masar Husni Mubarak

21:06 - February 02, 2012
Lambar Labari: 2267206
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin yahudawan sahyuniya sun fara yin kira da a saki Husni Mubarak tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Masar wanda yanzu haka yake fuskantar shari’a bisa zarginsa da kashe masu zanga-zangar lumana a kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dilalncin labaran Nun cewa, wasu daga cikin yahudawan sahyuniya sun fara yin kira da a saki Husni Mubarak tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Masar wanda yanzu haka yake fuskantar shari’a bisa zarginsa da kashe masu zanga-zangar lumana a kasar a lokacin juyin juya hali wanda ya kawo karshensa.
An gudanar da wani babban taron cika shekara guda da samun nasarar juyin juya hali a kasar Masar wanda ya kai ga kifar da gwamnatin kama karya ta tsohon shugaban kasar Husni Mubarak daga mulkin kasar ta Masar a jiya.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan babban taro ya kayatar matuka, bisa la’akari da cewa kasar Masar tana da matukar muhimamnci a cikin kasashen larabawa da kuma yankin nahiyar Afirka baki daya, wannane ma ya sanya yanzu haka kasashen larabawa da suke yin amshin shata ga siyasar turawa.
Rahotannin sun tabbatar da cewa, dubban daruruwan mutanen ne suka gudanar da wani babban taron cika shekara guda da samun nasarar juyin juya hali a kasar Masar wanda ya kai ga kifar da gwamnatin kama karya ta tsohon shugaban kasar Husni Mubarak daga mulkin kasar ta masar mai dogon tarihi. 945359
captcha