Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kbwindow cewa, Isma’il Haniyya pira ministan palastinu a yuankin Gaza ya bayyana cewa al’ummar palastinu suna gab da samun nasarar kwato masallacin Qods baki daya daga danniyar yahudawan sahyuniya wadanda suke hankoron rusa shi da kuma kawar da sauran dukaknin alamomi na musulmi.
Haniyya ya byayana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi ga al’ummar kasar Tunisia a ziyarar da yake gudanarwa a wasui daga cikin kasashen yankin da suka hada Masar da kuma Suda gami da Turkiya, inda yake jadda matsayin kungiyar gwagwarmaya ta Hamas wajen ci gaba da yin gwagwarmaya domin samun ‘yancin al’ummar yankin.
Pira ministan yankin gaza a Palastinu Isma’il Haniyya ya bayyana cewa, yankin gabas ta tsakiya ya zama wani wurin buga misali da gwagwarmayar neman ‘yanci da fita daga karshin mulkin zalunci da kama karya azzaluman shugabanninsu da suke azurta kansu da dukiyoyin da al’ummar kasar suke da su.
A wani bangaren kuma ya naklato daga shafin sadrawa na yanar gizo na CPI cewa, kungiyar kasashen musulmi ta yi kakkausar suka da yin Allawadai da haramtacciyar kasar Isra’ila kan harin ta’addancin da ta kai masallatan musulmi palastina a cikin yankunan gabar yamma da kogin Jordan a cikin wannan mako.
959808