IQNA

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya A Afghanistan Ya Bukaci A hukunta Masu Cin Zarafin Kur’ani

20:26 - March 03, 2012
Lambar Labari: 2284717
Bangaren kasa da kasa, wakilin musamman na majalisar dinkin duniya akasar Afghanistan ya bukaci da hukunta dukkanin wadanda suke da hannu a keta alfarmar kur’ani mai tsarki a kasar tare da kuran kungiyar tsaro ta NATO da ta gaggauta yin hakan.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na xinhuwa nba kasar China cewa, John Cobis wakilin musamman na majalisar dinkin duniya akasar Afghanistan ya bukaci da hukunta dukkanin wadanda suke da hannu a keta alfarmar kur’ani mai tsarki a kasar tare da kiran kungiyar tsaro ta NATO da ta gaggauta yin hakan domin kawo karshen wutar rikicin da hakan ya jawo.
Jami’in ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya gudanar a birnin Kabul na kasar, inda ya ce hakika abin da ya faru keta alfarmar kur’ani ne wanda kuma hakan ko shakka babu keta alfarmar duk wani musulmi ne aduniya, daboda hakan wadanda suka yi wannan mummunan aiki ne suke da laifi, kuma hukunta ne su kawai zai kawo karshen bala’in da hakan ya jawo a kan nato da dakarunta a kasar Afghanistn.
A cikin wani bangaren jawabin nasa ya bayyan acewa, farmakin da masu zanga-zanga cikin fushi suka kai kan ofisoshin majalisar dinkin duniya a yankin Kanduz, ya sanya su barin yanki ba arziki, amma dag abisani za su koma domin ci gaba da ayyukansu a yankin.
963655



captcha