Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: an fara bada horo kan sanin karanta kur'ani mai karfi da kuma tafsirin kur'ani mai girma a jami'ar mata ta Zahra a kauyen Radawi da ke garin Karaci na kasar Pakistan . Dahira Fadili shugabar wannan jami'ar mata ta Zahra (AS) a wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ta bayyana cewa; wannan bazarar bada horo kan sanin karatun kur'ani mai girma da kuma tafsiri tun daya ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ne aka fara kuma za a ci gaba har zuwa cikin watan Farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya. Har ila yau shugabar wannan jami'ar ta kara da cewa ana koyar da tajwidi da tarjamar kalmomi nba kur'ani mai girma ga manyan mata kuma daga karshen wannan horo za su samu shahada daga mu'assisar Tanzilul Kur'ani.
965363