IQNA

Bawa Sojojin Nato Horo Kan Mutuntawa Da Girmama Kur'ani

18:13 - March 10, 2012
Lambar Labari: 2289004
Bangaren kasa da kasa: a daidai wannan lokaci da musulmi a fadin duniya ke ci gaba da nuna adawarsa da yin Allah wadai da babbar murya kan sojojin mamaye na Amerika a Afganistan da suka muzanta kur'ani mai girma ,mahukumatn kungiyar tsaro ta Nato a Afganistan sun dauki wani mataki na gyara kayanka na bawa sojojinsu da Afganistan wani horo na musamman mai taken girmama Kur'ani mai girma.



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a daidai wannan lokaci da musulmi a fadin duniya ke ci gaba da nuna adawarsa da yin Allah wadai da babbar murya kan sojojin mamaye na Amerika a Afganistan da suka muzanta kur'ani mai girma ,mahukumatn kungiyar tsaro ta Nato a Afganistan sun dauki wani mataki na gyara kayanka na bawa sojojinsu da Afganistan wani horo na musamman mai taken girmama Kur'ani mai girma. An jiyo daga jaridar News da ake buga ta a kasar Pakistan cewa; wannan bada horo na musamman na tsawon mako guda ne da kuma aka fara shi da burin hana sake abkuwar abin day a faru na muzanta kur'ani da wasu sojojin mamaye na Amerika suka yi a birnin Kabul fadar mulkin kasar Afganistan .Janar Jorg Rabinson daya daga cikin komandodin sojon ruwa na Amerika da kuma ke bangaren yare da al'adu na rundunar sojin rowan na amerika ya shaidawa jaridar Los Anjals Taimes kan wannan lamari cewa: a wanna horo za a shaidawa sojojin ko suna so ko bas u so dole su girmama ur'ani mai girma littafin da musulmi ke girmamawa kuma za a shaida masu dalilin day a sa musulmi ke girmama kur'ani.Ya jaddada cewa rashin sanin larabci da sojojin kle fama dashi za a shaida masu cewa dole ne su girmama duk wani abu da suka gani da larabci gudun kar su fada sake aikata aikin gaganci da suka aikata na kona kur'ani masu tsarki a kasar Afganistan . masu lura da abubuwa da ke faru sun shaida cewa irin gagaramin martini da fushin da musulmin duniya da gwamnatoci da hukumomin duniya ne ya tilastawa mahukumtan sojojin na kungiyar tsaro ta Nato da hadin guiwar na Amerika daukan wannan mataki na bawa sojojinsu horo kan girmamawa da dajarta kur'ani mai tsarki.
968249
captcha