IQNA

An Sanyawa Wata Rana Sunan Girman Kur'ani Mai Girma A Pakistan

18:16 - March 11, 2012
Lambar Labari: 2289839
Bangaren kasa da kasa; al'ummar musulmi a Pakistan a wannan lokaci na maida martini kan cin zarafin da sojojin mamaye na Amerika suka yi wa Kur'ani mai girma a birnin Kabul fadar mulkin kasar Afaganistan a ranar sha tara ga watan Isfand sun sanya wa wannan rana ta juma'a suna n girman kur'ani mai girma tare da yin Allah wadai da babbar murya kan sojojin kungiyar tsaro ta Nato.


Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: al'ummar musulmi a Pakistan a wannan lokaci na maida martini kan cin zarafin da sojojin mamaye na Amerika suka yi wa Kur'ani mai girma a birnin Kabul fadar mulkin kasar Afaganistan a ranar sha tara ga watan Isfand sun sanya wa wannan rana ta juma'a suna n girman kur'ani mai girma tare da yin Allah wadai da babbar murya kan sojojin kungiyar tsaro ta Nato.Bayan kammala salalr juma'a birane daban daban na faddin kasar ta Pakistan musulmi sun fito domin yin Allah wadai da wannan mummunan aiki na takalar fada da suka yin a kona kur'anai da gangan domin haddasa fitina a kasar Afganistan inda musulmi a kasar ta Afganistan da sauran biranai da kasashe na musulmi suka yi ta yi masu Allah wadai da tofin Allah tsine .Su ma musulmin Pakistan sun fito a wannan rana ta juma'a da ta gabata domin yin Allah wade da sanya wa wannan rana sunan girmama kur'ani mai girma.


968985
captcha