IQNA

Ayoyin Kur'ani Za Su Zayyana Guraren Sanarwa Na Jirgin cikin karkahin Kasa A Amerika

13:52 - March 12, 2012
Lambar Labari: 2290360
Bangaren kasa da kasa:jam'iyar musulunci ta Boston na Amerika a burinta na yakar masu tsananin ra'ayin addinin musulunci da kuma bayyanawa da fayyace kyakkyawar fuskar musulmi da addinin musulunci ta yi niyar sanya ayoyi masu galgadi da nasiha da kuma kashedi a guraren kafa sanarwowi da isar da soko na tashoshin jiragen cikin karkashin kasa a Amerika.


Kamfanin dillancin labarai na iKna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: jam'iyar musulunci ta Boston na Amerika a burinta na yakar masu tsananin ra'ayin addinin musulunci da kuma bayyanawa da fayyace kyakkyawar fuskar musulmi da addinin musulunci ta yi niyar sanya ayoyi masu galgadi da nasiha da kuma kashedi a guraren kafa sanarwowi da isar da soko na tashoshin jiragen cikin karkashin kasa a Amerika. An jiyo daga majiyar labarai ta Mooslym cewa: jam'iyar musulmi yankin Boston na kasar Amerika ta yi niyar da burin ganin ta jawo hankalin al'ummar garin da fadakar das u cewa addinin musulunci ba addini ba ne na tashin hankali da tsautsoran ra'ayin riko illa addini ne ta sulhu da kwanciyar hankali da walwalai,kuma addini ne mai son zaman lafiya a tsakanin bangarori daban daban na musulmi da kuma sauran mabiya addinai na duniya duk wani mai son tada zaune tsaye da tashin hankali ko haddasa rikici da nuna tsautsoran ra'ayin riko ko ba ya aiki da umarnin addinin musulunci da kuma koyi da halayyar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa wanda ya rayuwa tare da kiristoci da yahudawa tare da kiyayae hakkokin kowa da kowa. Wannan jam'iya ta yi kuduri aniyar sanya ayoyin kur'ani na fadakarwa a guraren isar da sako na tashoshin jiragen cikin karkashin kasa a garin Boston na amerika shiriin da aka bawa taken Musulunci 101.
969824
captcha