Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya tsawa rahoton cewa: ma'aikatar kula da harkokin kur'ani a Jodan ta bayyana cewa; kasashe tara na duniya ne a halin yanzu suka bayyana cewa ashirye suke su turo wakilansu don halartar gasar karatun kur'ani mai girma ta kasa da kasa karo na ashirin da za a yi a kasar ta Jodan.Jaridar Aldastur da ake bugawa a kasar Jodan c eta watsa labarin cewa: Abdulsalam Al'ibadi ministan harkokin addini da kuma da gurare da abubuwa masu daraya na addinin musulunci ya bayyana cewa; ma'aikatarsa a kokari da niyarta ta shirya gasar karatun kur'ani da harta da kuma tafsirin kur'ani mai girma musamman ga maza ta mika goran gayyatar halartar wannan gasa karo na ashiri ga kasashe arba'in da daya na duniya kuma inji shi ya zuwa yanzu sun samu kasashe tara na duniya da suka amince za su aiko da turo da wakilansu domin halartar wannan gasa ta kasa da kasa ta karatun kur'ani da harda da kuma tafsiri karo na ashirin. Wannan gasar karatun kur'ani mai girma karo na shiri da kuma aka saba guidanarwa a kasar it ace matsayi na bakwai a tsakanin irin gasar karatun kur'ani da ake gudanarwa a duniya baki daya.
974976