Bangaren kasa da kasa, an fara gudamar da wani taron baje koli na dardumar nafis a birnin paris na kasar Faransa da ke dauke da ayoyin kur’ani mai tsarki, wanda ke samun halartar mutane musulmi da ma wadanda ba musulmi da suke da shawar sabnin wani abu dangane da addinin muslunci.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, an fara gudamar da wani taron baje koli na dardumar nafis a birnin paris na kasar Faransa da ke dauke da ayoyin kur’ani mai tsarki, wanda ke samun halartar mutane musulmi da ma wadanda ba musulmi da suke da shawar sanin wani abu dangane da addinin muslunci lamarin da aka bayyana shi da cewa ya kayatar matuka.
A wani rahoton na daban kuma jam’iyun adawa uku na masu kishin islama a kasar Algeria sun sanar da kafa wata babbar hadaka domin fuskantar zabuka masu a kasar da nufin kayar da jamiyya mai mulki a halin yanzu a kasar karkashin jagorancin shugaba Butaflika.
Wadannan jamiyu wadanda suka shafe tsawon lokaci suna adawa sun samu dama a wannan lokaci da ake bore a cikin wasu kasashen larabawa domin kawar da gwamnatoci ‘yan kama karya da suke yin amshin shata ga Amurka, misali daga ciki kuwa shi ne abin da ya faru akasar Masar, inda aka kawar da tsohon shugaban mulkin kama karya dan koren Amurka, kuma masu kishin islama suka mamaye sha’ann mulki.
jam’iyun adawa na masu kishin islama a kasar Algeria sun dai sanar da kafa babbar hadaka ne domin fuskantar zabuka masu a kasar da nufin kayar da jamiyya mai mulki, duk kuwa da cewa masu kishin islama da suka samu mulki a Tunisia da Libya sun bayan da mummnan misali, inda suka mika kai ga turawan yamma.
989975