Bangaren kur'ani, ana samun ci gaba wajen kafa cibiyoyin addinin muslunci da na kur'ani a kasar Brazil wanda musulmi mazauna kasar waanda akasarinsu sun fito ne daga kasashen larabawa suke kafawa domin amfanin mabiya addinin muslunci da ke kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, a cikin lokutan nan dai ana samun ci gaba wajen kafa cibiyoyin addinin muslunci da na kur'ani a kasar Brazil wanda musulmi mazauna kasar waanda akasarinsu sun fito ne daga kasashen larabawa suke kafawa domin amfanin mabiya addinin muslunci da ke kasar domin amfaninsu.
A wani labarin kuma yan siyasa da kuma kungiyoyi daban daban a ciki da kuma wagen kasar Bahrain suna ci gaba da sukar shawarar sarakunan kasashen saudia da Bahrain na dunkulewar kasashen saudia da Bahrain su zama kasa kuda, Duk da cewa majalisar kungiyar kasashen larabawa ta yankin tekun farisa ta yi watsi da shawarar dunkulewan kasashen biyu a wani taron da suka gudanar a cikin wannan watan da muke ciki, amma Sarakunan Aali Khalifi da kuma Aali sa'ud sun dage kan dunkulewar kasashen biyu.
Masana da dama suna ganin, burin sarakunan wadannan kasashe biyu da wuya ya kai labara don wasu dalilai da dama, na farko don ganin hadewar kasashe biyu ba wani abu ne wanda sarakuna ko shuwagabbannin wadan nan kasashe zasu zauna su zartar da abinda suka ga dama ba ne. Har'ila yau hadewar wadanan kasashe biyu yana bukatar jin ra'ayin mutanen wadannan kasashe, wato dole ne a gudanar da zaben jin ra'ayin musamman ga mutanen kasar Bahran kafin wannan lamarin ya tabbata.
1013367