IQNA

Wasu Ta’adda Sun Kaddamar da Hari Kan Taron Tunawa Da Shahadar Imam Ali (AS)

14:41 - August 11, 2012
Lambar Labari: 2390239
Bangaren kasa da kasa, sakamaon wani harin ta’addaci da aka kai kan masu gudanar da taron tunawa da zagayowar ranar shahadar Imam Ali (AS) a kasar Iraki mutane 50 suka yi shahada da kuma samun raunkua a yunkurin da mabiya tafarkin wahabiyanci suke na ganin cewa sun hana gudanar da duk wani tarin ibada da ya shafi iyalan gidan manzo.
Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Iba, cewa sakamaon wani harin ta’addaci da aka kai kan masu gudanar da taron tunawa da zagayowar ranar shahadar Imam Ali (AS) a kasar Iraki mutane 50 suka yi shahada da kuma samun raunkua a yunkurin da mabiya tafarkin wahabiyanci suke na ganin cewa sun hana gudanar da duk wani tarin ibada da ya shafi iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da layensa tsarkaka.
Shi kuwa a nasa bangaren Sheikh Hassan Saffar daya daga cikin malaman addinin muslunci a kasar Saudiyya ya bayya cewa a koda yaushe mabiya tafarkin iyalan gidan manzon ne hare-haren ta’addanci ke nufa a kasashen duniya musamman ma a cikin kasashen larabawa da suke yankin gabas ta tsakiya da kuma kasashen da suke makwaftaka da su wadanda su ma suke sheda irin wadannan ayyuka.
Ya ci gaba da cewa wannan bas hi karon farko da mabiya tafarkin iyalan gidan amnzon Allah suka fara fusknatar zalunci daga azzaluman sarakuna ba, kamar yadda bas hi karon farko da suke fuskantar zalunci daga mutanen da suka samu karkatar sahihin tunani da akidar muslunci, wadanda suike kafirta kowa tare da daukar cewa su kadai ne musulmi, ya ce a tarihin limaman gidan manon Allah cike da hakan.
1075023
























captcha