Bangaren kasa da kasa, a karon farko tashar talabijin din kur’an ta watsa shirinta daga hubbaren Imam Hussain (AS) da ke birnin Karbala mai alfarma a kasar Iraki kai tsaye wanda hakan ya zama daya daga cikin muhimman ayyuakan da wannan tasha ta gudanar tun daga lokacin da aka kafa.
Kmafanin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa a karon farko tashar talabijin din kur’an ta watsa shirinta daga hubbaren Imam Hussain (AS) da ke birnin Karbala mai alfarma a kasar Iraki kai tsaye wanda hakan ya zama daya daga cikin muhimman ayyuakan da wannan tasha ta gudanar tun daga lokacin da aka kafa a hukumar talabijin da radio ta jamhuriyar muslunci.
Ana shirin gudanar da wata gasa kan muhimman abubuwan da addinin muslunci ya ginu a kansu wadda ta kebanci matasa mabiya addinin muslunci na kasar wadda za ta gudana a birnin Rayazan na kasar tare da halartar malaman addini da kuma masana da shugabannin cibiyoyi.
Bayanin ya ce an bude wani masallaci a cikin bababr hedikwatar ‘yan sanda da ke birnin Bankok fadar mulkin kasar Thailand a wani mataki na kara tabbatar da mabiya addnin muslunci da ke kasar a matsayin daya daga cikin mabiya addinai sannu a kasar wadda akasarin mabiya addinain buda.
1080010