Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa an gudanar da wani zaman taro domin nazari kan matsayin jihadin Imam Sadiq a dukkanin bangarori da suka hada da irin gagarumar gudunmawar da ya bayar wajen yada ilimin addinin muslunci da fikihunsa ga al’ummar musulmi wanda ya samu halartar malai da kuma masana daga sassa na kasashen musulmi.
Fiye da shekaru 30 da suka gabata ne Imam Khomaini (q) wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya ayyana ranar jumma’a ta karshe na watan na Ramadan na ko wace shekara da ta zama ranar Qudus ta duniya, ranar da musulmi a nan kasar Iran da kuma sauran kasashen duniya zasu daga muryoyinsu da nunan goyinbayansu ga al-ummar kasar Palastinu wadanda ake zalanta. Jagoran juyin musuluncin ya kara da cewa, a cikin yan shekarun da suka gabata,
Kasashen yamma musamman Amurka da Ita HKI sun yi kokarin ganin sun mantar da al-ummar musulmi batun Palasdinu da kuma zaluncin da yahudawan Sahyoniyya suke musu, ta hanyar kokarin samar da sulhu, da kasashe biyu na al-ummu biyu ta Palasdinawa da kuma yahudawan sahyoniyya, Amma habakar da raya ranar Qudsu take samu a ko wace shekara da kuma borin farkawar Musulunci wanda ya taso koma ya ci gaba da faruwa a kasashen musulmi da dama a yankin gabas ta tsakiya, ya sake farfado da baton kasar Palasdinu, ya kuma maida shi matasala mafi muhimmanci ga al-ummar musulmin a duka fadin duniya.
An gudanar da zanga zangar ranar Qudsu ta duniya ne a ranar jumma’a da ta gabata a cikin kasashen duniya kimani 70, inda musulmi masu azumi suka daga muryoyinsu suka yi ta kira da aka kawo karshen mamayar kasar Palasdinu suka kuma yi tir da manya manyan kasashen duniya masu goyawa yahudawan sahyoniyya baya kan mamayar da suke wa kasar Palasdinawa. A wani bangare na jamwabinsa jagoran juyin Musulunci, ya yaba da yadda sauran musulmi a wasu kasashen duniya suka kara shigowa don raya wannan rana, don ganin al-ummar Palasdinu sun fita cikin halin da suke ciki na zalunci.
Jagoran ya kara jaddada cewa, tafarki da kuma matakan da al-ummar musulmi a yankin gabas ta tsakiya suka dauka, tafarkin ne da ya dashe kuma ya bukace su da su ci gaba da ita. Ya kuma yi kira a garesu, da su yi hattara da makirci makircen makiya, musamman na kokarin jefa gaba da kiyyaya tsakanin al-ummar musulmi da nufin raba kansu, da kuma kauda su kan tafarkin da suke kai a halin yanzu. Aya. Sayyeed Aliyul Khaminaee yay i kira ga shuwagabannin gwamnatocin kasashen musulmi, musamman wadanda suka maye gurbin azzaluman shuwgabannin da suka shude. 1092418