IQNA

Gasar Karatun Kur’ani Mai Tsarki Ta Taimka Ma Matasa Da Dama Wajen komawa Ga Kur’ani

17:52 - September 11, 2012
Lambar Labari: 2409951
Bangaren kasa da kasa, gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki da ake gudanarwa a mataki na kasa da kuma na duniya ya taimaka ma matuka wajen karfafa gwiwar matasa wajen komawa zuwa ga karatu da kuma sanin ma’anonin ayoyin kur’ani mai tsarki a cikin kasashen musulmi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarat cewa, ya naalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki da ake gudanarwa a mataki na kasa da kuma na duniya ya taimaka ma matuka wajen karfafa gwiwar matasa wajen komawa zuwa ga karatu da kuma sanin ma’anonin ayoyin kur’ani mai tsarki a cikin kasashen musulmi daban-daban.
Bayanin ya ci da cewa daga cikin matasa masu halartar gasar da ake gudanarwa a matsayi na kasashen duniya akasarinsu sun tasirantu ne da gasar da suke ganin ana gudanarwa a kasashen musulmi, inda matasa suke bayar da gagarumar rawa awannan bangare kuma suke samun nasara wajen karatu da harda da taimakon Allah da kuma himar da suke nunawa.
Wannan gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki da ake gudanarwa a mataki na kasa da kuma na duniya ya taimaka ma matuka wajen karfafa gwiwar matasa wajen komawa zuwa ga karatu da kuma sanin ma’anonin ayoyin kur’ani mai tsarki a cikin kasashen musulmi na duniya.
1066330


captcha