Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam, cewa kungiyar daliban jamioin kasashen musulmi ta yi kakausar da yin Allawadai da cin zarafin addinin muslunci da aka yi a kasar Amurka wanda ya kasance ta hanayr fitar da wani fim na muzunta addinin muslunci da kuma manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi da iyalan gidansa tsarkaka.
Majalisar dokokin kasar Yemen ta bukaci sojojin Amurka su fice daga babban birnin kasar Sanaa.
Majalisar ta bukaci ficewar sojojin ne bayan sanarwan da gwamnatin kasar Amurka ta bayar da ke cewa ta aike da sojojinta zuwa birnin na Sanaa domin bayar da kariya ga ofishin jakadancinta a can, biyo bayan zanga zangar da mutanen birnin suka yi a harabar ofishin a jiya jumma’a. inda suke nuna fushinsu kan majigin nan na batunci ga manzon Allah.
Yansanda a kasar ta yemen dai sun kama mutane da dama sun tsare kan zanga zangar nuna fushin da suka yi kan batanci ga Musulunci.
Har’ila yau an gudanar da zanga zangar nuna fushi ga majigi mai batunci ga Musulunci a birnin Sudney na kasar Australia a gaban ofishin jakadancin kasar Amurca, Yan sandan gwamnatin Australia sun kama mutane da dama, wasu kuma sun samu raunuka a lokacin da yansanda suke kokarin tarwatsa su.
A nata bangaren majalisar dokokin kasar Afganistan ta yi Allah wadai da majigin wanda yake muzanta manzon Allah (s), kuma ta bukaci kasar Amurka ta haramta majaigin ta kuma gurfanar da wadanda suke da hannun wajen yin sa, kamar yadda majaliar ta bukaci da a janye dukaknin yarjeniyoyin tsaro da aka rattaba hannu kansu tsakanin Amurka da Afhanistan.
1099492