Kamfanin dilalcnin labaran iqna ya nakalto daga tashar Telbijin din al-Alam mai watsa shirye-shiryenta daga nan Tehran ta ce; Jami’an tsaro masu mulkin kasar al-Khalifa, sun murkushe masu Zanga-zangar lumana da su ka nufi dandalin lu’u-lu’a a tsakiyar babban birnin kasar Manama.
Har ila yau, Zanga-zangar da aka gudanar a cikin sassa-sassa daban- daban na kasar ma ta fuskanci amfani da karfi daga jami’an tsaro.
A tsibirin Sitrah, jami’an tsaron kasar sun hana gudanar da duk wani taro da kuma Zanga-zanga.
Zanga-zangar ta jiya ta zo ne a matsayin share fagen na Zanga-zangar da za a gudanar a yau alahamis domin tunawa da cika shekaru biyu daidai da farkon yunkurin al’ummar kasar.
Mutanen kasar Bahrain sun fara zanga-zangar neman hakkokinsu na siyasa a matsayinsu na 'yan kasa ne a ranar 14 ga watan Fabrairun shekara ta 2011, inda suka bukaci maarautar kasar da ta ci gaba da mulki, amma a baiwa al'ummar zabar mambobin majalisar dokoki da kansu, maimakon sarki ya nada wadanda ya ga dama ba tare da ra'yin al'umma ba.
1188808