IQNA

Mahukuntan Faransa na cin zarafin musulmi yankuna da dama na kasar

20:42 - March 04, 2013
Lambar Labari: 2506126
Bangraen kasa, wasu daga cikin mabiya addinin muslunci a kasar Faransa sun bayyana rashin gamsuwa da matakan da wasu mahukunta suke dauka a kasar na cin zarafin musulmi musamman a birnin paris fadar mulkin kasar, duk kuwa da alkawalin da shugaban kasar ya dauka na kare hakkokinsu.
Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, da dama daga cikin mabiya addinin muslunci a kasar Faransa sun bayyana rashin gamsuwa da matakan da wasu mahukunta suke dauka a kasar na cin zarafin musulmi musamman a birnin paris fadar mulkin kasar inda suke fuskantar tsangwama.
A wani rahoton kuma na daban gwamnatin kasar Faransa ta tabbatar da cewa an kashe sojanta guda daya a kasar Mali ammam bada tabbatar da kisan kamandan dakarun yan tawayen da suka yi garkuwa da ma’aikatan wani kamfanin iskar gas a cikin watan jenerun wannan shekarar ba, kamar yadda gwamnatin kasar Chadi ta bayyana.
Yakin makonni 7 wanda sojojin kasar Faransa suka kaddamar a raewacin kasar Mali dai ya tilastawa yan tawayen ercewa zuwa kan tsaunukan da ke iyakar kasar da kasar Mali, inda kuma sojojin kasashen na faransa Chadi da kuma Mali suke farautartu a can. Ma’aikatar harkokin tsaron kasar farasa ta bada sanarwan cewa Corporal Cedric Charenton dan shekara 26 da haihuwa ya mutu a wani musaya wuta a wani wuri kan tsaunukan da ke kusa da kasar Aljeria a jiya lahadi.
Kakakin ma’aikatar tsaron kasar ta Farasnas Colonel Thierry Burkhard ya kara da cewa yan ta’adda 15 ne suka mutu a musayar wutan na jiya, sannan ya ce bai da tabbacin cewa an kashe shugan wadanda suka yi garkuwa da yan kasashen waje a kamfanin iskar gasa na kasar Aljeria a cikin watan Jenerun da ta gabata wato Mokhtar Belmokhtar ba, wanda gwamnatin kasar Chadia ta bayyana.
1198900


captcha