Bangaren kasa da kasa, daya daga cikin malaman addinin muslunci daga bangaren yan sunna a kasar Lebanon ya bayyana cewa Iran da kungiyar hizbullah babu wani laifi da suka yi ma mabiya tafarkin ahlu sunna amma kuma ana yaudararsu suna fada da su domin kawai su manta da Isra’ila kuma su kare bas u sani ba.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Ahmad Wahidi ya bayyana irin mu'amalar da kasashen yammaci suke yi da al'ummomin yankin nan a matsayin wata mu'amala ta yaudara da ha'inci.
Janar Wahidin ya bayyana hakan ne a yau din nan a lokacin da ya ke mayar da martani ga jawabin da ministan tsaron kasar Jamus Thomas de Maiziere ya yi na dalilan da suka sanya su sayar da makamai ga kasashen yankin Tekun Fasha inda ya ce wadannan maganganu ne da suke nuni da yadda kasashen yammacin suke wadanta da dukiyar wadannan kasashen don cimma manufarsu ta kare HKI.
Janar Ahmad Wahidi ya kara da cewa wadannan maganganu suna nuni da bakar aniyar da kasashen yammacin suke da ita a kan kasashen yankin nan, sannan kuma babu abin da suka sa a gaba in banda kare manufofinsu da kuma na HKI.
A kwanakin baya ne ministan tsaron kasar Jamus din Thomas de Maiziere ya bayyana cewar kasar Jamus tana sayarwa kasashen larabawan Tekun Fasha da makamai ne don kawo karshen abin da ya kira barazanar Iran da kuma kare HKI, inda ya ce a wajen kasar Jamus kare HKI daga barazanar Iran ya fi musu muhimmanci a kan take hakkokin bil'adama da ake yi a kasar Saudiyya
1199931