IQNA

An Kirayi magoya Bayan Kungiyar 'Yan uwa Musulmi Domin Yin Zanga-Zanga

23:17 - July 15, 2013
Lambar Labari: 2561997
Bangaren kasa da kasa, masu zanga-zangar dai suna dauke da kwafi-kwafi na alkur'ani mai tsarki a hannunuwansu na dama da kuma totocin kasar Masar a hannuwansu an hagu, inda suke rera taken halascin shugabancin kasar Masar yana ga Muhammad Morsi ne kawai.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, daya daga cikin jagororin kungiyar 'yan uwa musulmi Safwat Hijazi ya gabatar da jawabi mai tsawo a gaban dubban magoya bayan kungiyar, inda ya ce za su ci gaba da kasancewa a wurin ko da za su kai wata daya ko watanni biyu, har ma sheka ko shekaru biyu, har sai an dawo da Muhammad Morsi a kan shugabancin kasar Masar.

A cikin 'yan kawanakin da suka gabata ne jagoran kungiyar Muhammad Badi ya gabatar da jawabi a gaban magoya bayan kungiyar da suke zaman dirshan a masallacin Rabi'at Adwiyyah, inda ya shelanta cewa za su sadaukantar da kansu ta hanyar yin shahada a tafarkin dawo da Muhammad Morsi kan shugabancin kasar Masar, kwana guda bayan wannan jawabin ne wasu daruruwan magoya bayan kungiyar ta 'yan uwa musulmi suka kai samame kan wani babban gini na ma'aikatar tsaro da ake zaton cewa a wurin ne ake tsare da Muhammad Morsi, inda suka yi ba-ta-kashi tsakaninsu da sojojin da ke gadin wurin, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar magoya bayan kungiyar fiye da 40, da kuma wani babban jami'in soji guda tare da jikkatar wasu.

A nasa bangaren Firayi ministan rikon kwaryar kasar ta Masar Hazim Bilawi ya fadi a jiya Juma'a cewa, yana ci gaba da tattaunawa da bangarorin siyasar kasar domin kafa gwamnati, inda ya ce yana sa ran fara tattaunawa da mutanen da za su rike mukaman ministoci a ranar Lahadi ko Litinin mai zuwa, ya ce babu abin da zai hana kungiyar 'yan uwa musulmi shiga cikin gwamnatin rikon kwaryar da za a kafa, amma tuni kungiyar ta yi watsi da wannan batu.

Da dama daga cikin masana da kuma 'yan siyasa a kasar ta Masar da hakan ya hada har da su kansu 'yan kungiyar 'yan uwa musulmi, sun gamsu da cewa Muhammad Morsi ya tafka kurakurai da suka jawo matsaloli masu tarin yawa ga kasar a cikin shekara guda da ya yi yana mulki, to amma ra'ayoyi sun banbanta kan yadda ya kamata a tunkari lamarin, amma masu adawa da shi suka fifita gudanar da zanga-zangar nuna kiyayya da salon mulkinsa a fadin kasar daga ranar 30 ga watan Yunin da ya gabata, wadda aka bayyana ta da cewa ita ce zantaga-zanga mafi girma da aka taba gudanarwa a tarihin kasar ta Masar, wanda kuma hakan ne ya bai wa sojoji damar hambarar da shi daga kan karagar shugabancin kasar, bisa hujjar gazawarsa wajen gudanar da ayyukan da kasa da al'ummarta suke bukata, da kuma yin watsi da kiraye-kirayen a kasarin al'ummar kasar Masar a kansa.

1258410







captcha