Kamfanin dilalncin labaran iqna ya ce alummar musulmi a duniya sun yi Allawadai da kai harin ta'addanci kan hubbaren sayyida Zainab kasar Syria wanda yan ta'adda da ke samun goyon bayan amurka da larabawa suka yi tare da goyon bayan uwayen gidansu.
Rahotanni daga kasar Syria na nuni da cewa mayakan kungiyar alkaida sun kame daruruwan fararen hula suna garkuwa da su a garin Tal Abyad da ke arewacin kasar, a wani mataki na mayar da martani kan kame babban jigon kungiyar kuma shugaban abin da take kira daular Musulunci a Iraki da sham, da mayakan Kurdawa suka yi a jiya.
Wata cibiya da ke kusa da masu tayar da kayar baya a Syria da ke kiran kanta cibiyar kare hakkin bil adama a Syria da ke da mazauni a birnin London na kasar Birtaniya ta fadi yau cewa, mayakan na alkaida sun yi garkuwa ne da daruruwan faraen hular domin neman a saki shugaban nasu Abu Mus'ab , wanda a yau mayakan Kuradawan suka sake shi.
Al'ummar garin Tal Abyad da suka hada da Kurdawa da kuma mabiya mazhabar shi'a da 'yan sunna da ma kiristoci, sun kwashe daruruwan shekaru suna rayuwa tare da juna lami lafiya, amma yakin da aka haddasa a kasar Syria ya tarwatsa al'ummar garin, inda akasarinsu a halin yanzu sun zama 'yan gudun hijira.
A ranar Juma'ar da ta gabata ce dai 'yan ta'adda da ake kira 'yan tawayen Syria suka harba makaman roka kan hubbaren Sayyida Zainab (AS) diyar Fatima Zahra (AS) diyar Manzon Allah (SAW) wanda ke kusa da birnin Damascus, wannan harin kuwa ya zo ne kwana daya bayan sanarwar da 'yan ta'adda suka bayar cewa sun samu manyan makamai da daga wasu gwamnatocin larabawa.
1261206