IQNA

‘Yan ta’adda sun kai hari kan jami’an majalisar dinkin duniya a Syria

17:22 - August 27, 2013
Lambar Labari: 2581280
Bangaren kasa da kasa, wasu ‘yan bindiga sun kai wa tawagar wakilan Majalisar dinkin Duniya hari wandanda suka shiga kasar domin gudanar da binciken harin makamai masu guba da ake zargin an yi amfani da su a rikicin kasar. Kakakin Majalisar Dinkin Duniya Martin Nesirky yace wakilan sun fice daga yankin.
A cewar Nesirky, babu wani rahoton rauni da aka samu bayan an kai wa motar da ke dauke da tawagar hari a yankin Ghauta da ke gabas da Damascus. Nesirky yace wasu ‘Yan bindiga ne da ba a tantance ba suka bude wa tawagar wuta daga nesa. A yankin Ghauta ne aka ruwaito daruruwan mutane sun mutu sakamakon zargin yin amfani da makamai masu guba, inda kasashen Turai ke zargin dakarun Gwamnatin Bashar al Assad da alhakin kai hare haren, yayin da kuma gwamnati ke zargin ‘Yan tawaye. Akan haka ne kuma Majalisar Dinkin Duniya ta aika da wakilai domin gudanar da bincike.
Mataimakin babban komandan sojojin kasar Iran General Masoud Jazayeri ya yi kashediwa gwamnatin kasar Amurka kan wuce gona da iri a yakin da ke faruwa a kasar Syria.
Jazayeri, ya bayyana haka ne a yau lahadi ya kuma kara da cewa, duk wani kokarin da kasar Amurka zata yi na shiga da karfi a kasar Syria zai zame mata asara babba.
Mataimakin komandan yana maida martani ne ga maganar Chuck Hagel saketaron tsaron kasar Amurka a ranar 25 ga watan Augusta da muke ciki, inda yake bayyana cewa gwamnatin Amurka tana shirye shiryen amfani da karfi a kasar Syria.
Jazayeri ya kara da cewa a halin yanzu sojojin kasar Syria suna samun nasarori kan yan ta’adda masu samun goyon bayan kasashen yamma da kuma wasu kasashen yankin.

1279054



captcha