Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sautul Manama cewa, a daren jiya jami'an tsaron sarkin kasar Bahrain sun sake kaddamar da farmaki kan gidan babban malamin mabiya mazhabar shi'a na kasar Ayatooah Isa Kasim tare da cin zarafinsa da kuma keta alfarmar iyalansa.
Al’ummar kasar ta Bahrain sun gudanar da zanga-zanga don nuna bacin ransu kan wannan samame da Jjami’an tsaron kasar suka kai a gidan babban malamin na shi’a Sheik Isa Kasim, inda a jiya da da dare jami’an tsaron suka kai samame a gidan babban malamin a yayin da suka je gidansa basu samu babban malamin a gida amma sun kuble iyalansa cikin wani daki inda su kayi gaggaran bincike a gidan sannan sun ba ta abubuwa da dama a gidan nasa.
A kwanakin baya ma Gwamnati tayi barazanar kashe wannan babban malamin, al’ummar kasar Bahrain ta ja kunnan Gwamnati da kadda ta sake irin wannan cin mutunci ga wannan babban malami inda tace duk abinda ya samu wannan malami to alhakinsa na wuyan Gwamnatin.
Yanzu haka dai jama'a a ciki da wajen kasar ta Bahrain na ci gaba da yin Allawadai da kakakusar kan wannan aiki na dabbanci da 'yan bangar masarautar ta Bahrain suka aikata tare da umarnin iyayen gidansu, da nufin murkushe mabiya tafarkin iyalan gidan manzo.
2611618