Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-ahd cewa 'yan sanda kasa da kasa wato interpol na neman Yusuf Qardawi domin kame shi, mutumin da ke kara rura wutar ta'addanci a duniya, dukkanin mutanen da ake nema dais u 42 ne kamar yadda sanarwar ta tabbatar.
Hukumar ‘yan sandan duniya ta Interpol ya sanya babban malamin addinin musuluncin nan dan asalin kasar Masar Yusuf Qardawy a cikin jerin mutanen da ta ke nema ruwa a jallo. A yau asabar ne hukumar ‘yan sandan ta kasa da kasa ta sanar da shigar da sunan Yusuf Qardawy a cikin jerin sunayen mutanen da ta ke hankoron kamawa bisa bukatar da gwamnatin kasar Masar ta gabatar ma ta.
Shafin bayanan hukumar ‘yan sandan na internet ya sanya hotun Yusuf al-Qardawy da kuma tarihin ahihuwarsa da takardun kasashe da ya ke dauke da su, wato Masar da katar, tare da bukatar a tura mata karin bayanai akan laifukan da ake zarginsa da su, da su ka hada da kisan jama’a da sace mutane da fitar da fursunoni daga kurkuku. Sheikh Yusuf Qardawi dai fitattacen malamin addinin Musulunci ne wanda ya ke zaune a ksar katar.