Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Shafaq News cewa, a cikin wannan mako cibiyar kira da yada al’adun addinin muslunci a duniya wadda ke da mazauni a kasar Masar ta kori Yusuf Qardawi daya daga cikin masu taka rawa wajen yada ayyukan ta’addanci a koina da sunan addini.
Ita ma anta bangaren cibiyar gudanar da bincike kan harkokin addinin Musulunci a jami’ar Azhar ta kasar Masar ta sanar da korar Sheikh Yusuf Qardawi daga cibiyar, dukkan mambobin kwamitin cibiyar gudanar da bincike kan harkokin addinin Musulunci ta Islamic Research Academy da ke kasar Masar karkashin jagorancin shugaban jami’ar sun kada kuri’ar korar Sheikh Yusuf Qardawi daga kwamitin saboda matsayin da ya dauka na rashin mutunta kasar Masar da al’ummarta gami da cin mutuncin da yake yi ga shugaban jami’ar Azhar Sheikh Ahmad Tayyib.
Malamin koyar da shari’ar Musulunci a jami’ar Azhar ta kasar Masar ya bayyana Sheikh Yusuf Qardawi da cewa ya zama kakakin Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila tare da goyon bayan sarakunan kasashen Larabawa da suke kare munanan manufofin kasashen yammacin turai.
A cikin makon da ya gabata ne dai hukumar ‘yan sanda kasa da kasa ta Interpol ta sanar da cewa Yusuf Qardawi na cikin jerin sunayen mutanen da take nema domin ta kame shi.