Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga Darul kur’an Karim cewa wannan babbar cibiya ta bayyana cewa tana rarraba kwafi-kwafin n kur’ani mai tsarki da aka rubuta da knanan rubutu ga masu halartar tarukan ziyara na arba’in da suke isa birnin mai alfarma domin wannan ziyara.
Bayanai da dama dai sun tababtar da yanzu haka dai miliyoyin mutane daga cikin da wajen kasar suna ci gaba da tafiya zuwa birnin karbala na kasar Iraki domin halartar tarukan Arba'in na shahadar Imam Hussain (AS) da za a gudanar hubbarensa da ke birnin.
Da dama daga cikin masu aiko ma tashoshi rahotanni daga kasar Iraki ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu dai miliyoin mutane suke tafiya a kasa daga sassa daba-daban na kasar Iraki a kan hanyarsu ta isa birnin na Karbala, kamar yadda baki daga kasashen ketare suke isa kasar ta Iraki a iyakokinta na kasa da kuma filayen safkar jiragen sama a biranan kasar.
To amma kuma a nata bangaren rundunar 'yan sanda a kasar ta sanar da kammala daukar dukkanin matakan da suka dace domin bayar da kariya ga masu tarukan na addini, inda yanzu haka jami'an tsaro na hadin gwiwa tsakanin sojoj da 'yan sanda fiye da dubu uku suke ciki da wajen birnin na Karbala suna gudanar da ayyukansu na tsaro domin tababtar da cewa suna bayar da kariyar da ta kamata.