
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Almayadeen da ke watsa shirinta daga kasar Lebanon cewa, a cikin wani bayaninsa Matran Atallah Hanna jagoran mabiya addinin kirista a birnin quds ya yi kakkausar suka dangane da keta alfarmar wurare masu na musulmi da yahudawa suka shahara da yin hakan.
Haka nan kuma jagoran mabiya addinin kirista ya yi zuwa ga hadin kai tsakanin mabiya addinin mulunci da kiristanci domin fuskantar yahudawan sahyuniya, inda ya bayyana cewa barazanar ba ta takaita da wani bangare ta bar wani bangare ba, dukkanin musulmi da kiristoci na fuskantar barazanar yahudawan sahyuniya baki daya.
Ya kara da cewa duk da irin makircin da yahudawan ke yi domin rusa masallacin Quds mai alfarma, masallacin zai ci gaba da zama mallakin al’ummar larabawa har abada.
2618839