IQNA

Isra'ila Ta Ce Ba Za Ta Amince da Kafa Kasar Palastinu Mai Cin Gishin kai Ba

16:42 - December 19, 2014
Lambar Labari: 2622019
Bangaren kasa da kasa, Benjamin Netanyahu firayi ministan haramtacciyar kasar Isra'ila ya ce ba za su taba amincewa da duk wani shiri na kafa kasar Palstiu mai cin gishin kanta ba.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Maa cewa, a barazanar da yake yi firayi ministan haramtacciyar kasar Isra'ila ya ce ba za su taba amincewa da duk wani shiri na kafa kasar Palstiu mai cin gishin kanta ba matukar dai akwai daular yahudawan sahyuniya a kasa.

Kafofin yada labarai da dama a haramtacciyar kasar Isra'ila suna ci gaba da yin sharhi dangane da daftarin kudirin da kasashe larabawa suka mika wa kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya da ke neman amincewa da kasar Palastinu mai cin gishin kanta.
Firayi ministan haramtacciyar kasar Isra'ila Benjamin Natanyahu ya ce yana tabbaci a kan cewa Amurka ba za ta taba barin kwamitin tsaron majlaisar dinkin duniya ya amince da wannan daftarin kudiri, domin kuwa a cewarsa za ta hau kujerar naki kan wannan batu na kafa kasar Palastinu mai cin gishin kanta.
A ganawar da ta gudana jiya tsakanin sakataren wajen kasar Amurka John Kerry da babban mai shiga tsakani na gwamnatin palastinawa Said Uraikat, John Kerry ya bukaci gwamnatin Palastinawa ta janye daga duk wani batun kafa kasar Palstinu, idan kuma ba haka to kuwa Amurka za ta kakaba wa gwamnatin ta Palastinawa ta kunkumi.
2621938

Abubuwan Da Ya Shafa: palastine
captcha