IQNA

Dalibar Jami'ar Canada: Hijabi Na Bani Kariya Da Aminci

16:56 - December 20, 2014
Lambar Labari: 2623534
Bangaren kasa da kasa, Sofiya Malik wata dalibar jami'a akasar Canada ta bayyana saka jihabin mulsunci da atke yi da cewa yana bata kariya da kuma jin cewa tana cikin aminci a tsakanin al'umma.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Tronto Observer cewa, Sofiya Malik, wadda ita day ace daga cikin daliban jami'a  a kasar Canada ta bayyana saka jihabin mulsunci da take yi a rayuwartada cewa yana bata kariya da kuma jin cewa tana cikin aminci a tsakanin al'ummar da take rayuwa tare da su.
Dalibar ta ci gaba da cewa hijabi yana da matsayi na musamman wanda kuma babu wanda zai gane hakan sai wanda yake sakawa, domin kuwa baya ga suturci jikin mace da yake yi kamar yadda addini ya bukata kuma ya yi umarni, a bangare guda kuma babbar kariya ce ga m,ace da take rayuwa a cikin jama'a, domin kuwa yana bata mutunci da kima a tsakanin jama'a.
Ta ci gaba da cew kasantuwar daliba  ajami'a tana rayuwa  atsakanin sauran kawayenta dalibai ba tare da wata tsangwama ba, kuma bata ganin wani illa girmamawa daga dalibai da kuma su kansu malaman jami'ar, duk kuwa da cewa akasarinsu ba mabiya addinin muslunci ba ne, amma daga saka hijabi datake yi sun fahimci cewa ita ba mutuniyar banza ba, a kan hakan ko magana za ta hada su to za ta zama magana ce  acikin girmamawa.
Dangane da yanayin rayuwa acikin gari kuwa, ta ce ba ta fuskantar matsala daga matasa marassa tarbiya, kamar yadda sauran mata masu fitar da tsiraicinsu suke fuskanta a kasar, wanda kuma hakan ya zama ruwan dare a kasar baki daya.
2621905

Abubuwan Da Ya Shafa: canada
captcha