Kamfanin dillancin labaran Iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na aynar gizo na On Islam cewa, a kasashen Uganda da kuma Ethiopia mabiya addinin musulunci a kasashen sun gudanar da tarukan maulidin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a birane da dama na kasashen nasu, domin raya wanann lamari mai girma.
Wannan taro na maulidin manzo Allah da ake gudanarwa a kasashen Uganda da kuma Ethiopia yana da alaka ne da irin son muslunci da ke cikin zukatan al’ummomin wadannan kasashe kamar dai yadda lamarin yake a cikin tarihinsu.
A kowace shekara dai musulmi a dukkanin kasashen duniya suna gudanar da tarukan maulidin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a cikin kasashen msuulmi, har da kasashen da suke nuna tsananin adawa da wannan lamari da sunan addini, inda mabiya tafarkin iyalan gidan mazo da mabiya darikun sufanci suke gdanar da irin wadannan taruka.
Manzon Allah ya barwa al’ummare musulmi addinin mulunci cikkae tare da wasiyarsa ta yadda musulmi za su ci gaba da rayuwa kan sahihin tafarki, duk kuwa da cewa an yi watsi da wanann wasici jim kadan bayan da ya bar gidan duniya.
2672093