
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ina cewa, a lokacin ganarawarsa da Dawud Za’atari mai garin Alkhalil da ke Palastine, shugaban mabiya addinin kirista a birnin Quds ya yi Allawadai da jaridar da ke bata manzon Allah da cin zarafinsa, tare da tabbatar da cewa duk wanda ya keta alfarmar addinin muslunci to ya keta alfarmar addinin kirista ne kai tsaye ga duk wanda yay i hakan.
Ya ci gaba da cewa a lokacin gwamnatocin kasashen yamma suke son cimma wata manufa tasu sukan iya yin amfani da komai domin cimma wannan manufar, koda kuwa zai ci zarafin wasu ko wata akida ko addini, kuma za su yi hakan ne da sunan yancin fadar albarkacin baki, amma a lokacin da wani lamari ya shafe su sukan tsaya kai da fata domin su kare shi da kowane hujjoji.
Daga cikin misalan da ya bayar har da yada suke kare kisan yahudawa da aka yi a kasar Jamus tare da daukar kwararn matakai na shiga kafar wando daya da duk wanda yay i musun faruwar hakan a tarihi, kuma nuna shakku kan adadin da ake fada, inda yace babu adalcia a irin wannan mataki na ksashen yammacin turai.
2746322